iBet uBet web content aggregator. Adding the entire web to your favor.
iBet uBet web content aggregator. Adding the entire web to your favor.



Link to original content: http://ha.wikipedia.org/wiki/Sahur
Sahur - Wikipedia Jump to content

Sahur

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sahur

Sahur shine abincin da Musulmai ke ci a lokacin ɗaukar kowa ne irin Azumi galibi a cikin wata Ramadan, wanda ana yin Sahur ne a ƙarshen dare kafin fitowar alfijir sadiƙi wato kafin a kira sallah Asubah kiran karshe. Allah maɗaukakin sarki yana cewa a cikin Alqur'ani mai girma (فَالآنَ بَاشِرُوهُنَّ وَابْتَغُوا مَا كَتَبَ اللَّهُ لَكُمْ وَكُلُوا وَاشْرَبُوا حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَكُمُ الْخَيْطُ الأَبْيَضُ مِنَ الْخَيْطِ الأَسْوَدِ مِنَ الْفَجْرِ ثُمَّ أَتِمُّوا الصِّيَامَ إِلَى اللَّيْلِ[البقر:]187 Kuma Sahur sunnah ce ta Annabi Muhammad (S A W) don haka yanada matuƙar Muhimmanci. عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: “تسحروا فإن في السحور بركة “ عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم:قال “السحور بركة فلا تدعوه ولو أن يجرع أحدكم جرعة من ماء؛ فإنّ الله وملائكته يصلون على المتسحرين” Shi Sahur ba sai lokacin watan Ramadan ba koda Azumin Nafila ne anayin Sahur. Wato dai Sahur yanada lokaci keɓantacce da ake yinshi. Kishiyar Sahur shine buɗa baki (iftar) kenan shima anayin shine bayan rana ta faɗi kamar yadda aya Alqur'ani da ta gabata ta bayyana hakan, wato zuwa faɗuwa rana ba kamar yadda wasu suke cewa wai zuwa cikin dare bayan Isha'i ba. . Buɗa baki yana nufin abinda musulmi zai fara kaiwa a bakin sa so samune ɗanyen Dabino in kuma bai samu ba sai ayi da Ruwa Ko kuma abinda ya sawwaƙa. Allah shine masani.

Musaharati shi ne wanda yake tayar da mutane domin yin suhur da sallar asuba a cikin watan Ramadan. Kamar yadda littafan tarihi suka nuna, Bilal bin Rabah shi ne ɗan adam na farko a tarihin Musulunci, da ya fara yin aikin musaharati domin ya kasance yana yawo a kan tituna da hanyoyi tsawon dare don tada mutane Don kada su makara a lokacin sahur.[1] Wani dan kasar Damascus wanda shima aikin shi kenan a cikin tayar da mutane lokacin watan Ramadan. Har yake cewa "Aiki na shine in tayar da mutane a tsohon birnin Damascus don yin sallah da cin abincin sahur. A cewar Sidon sifofin Musaharati ya kamata su kasance, yana da koshin lafiya da lafiyayyan jiki, "domin aiki ne da ake bukatar shi da tafiya mai nisa kullum duk dare, sannan kuma ya kasance yanada karfin murya da lafiyayyen huhu, ya kuma kasance ya iya rear wasu wakoki da basu haramta ba a Musulunci wakoki, haka kuma Musaharati ya kasance yana raya dare da Ibadah (Nafilfili) da sauran su.

Ana yin al'adar a kasashe irin su Masar, Siriya, Sudan, Saudiyyah, Jordan, Indiya, Pakistan, Bangladesh, da Falasdinu. Sai dai kuma, a karnin baya-baya nan Al-adar musaharati a hankali ta bace saboda dalilai da dama, da suka hada da: Musulmai sun fara amfani da tekanolojin zamani; amfani da fasaha kamar agogon ƙararrawa (Alarm) don farkawa daga bacci a lokacin yin suhur; da manyan gidaje da garuruwa da suke kara sanya sautin sifiku na kiran sallah da musaharati ya fi karfin ji. Duk da haka, ana iya samun tsohuwar al'adar Dhakaiya ta rera qasidu akan titunan Old Dhaka a Bangladesh.[2]

A Indonesiya, ana amfani da kentongan don tada al'umman Musulmi dake cikin gidajensu don cin abincin suhur.

Musaharati a kasar Hausawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Haka a kasar Hausawa ana al-adar musaharati sai dai ya banbanta da suran kasashen musulmi. A kasar Hausa ana kiran musaharati da Tashe wato al-adar tashe wadda ake yinta a gomau biyu na karshen watan Ramadan. Kuma ita wannan al-adar a kasar hausa yara yan kasa da shekara goma sha biyar suke yinta, sabanin sauran kasashen da su mutum daya ne za'a zaba ko kuma zai saka kanshi don yin wannan al-adar ta tayar da mutane don yin sahur a lokacin watan azumi.[3]

Muhimmancin Sahur

[gyara sashe | gyara masomin]

Cin abinci da safe yana da matukar amfani da muhimmanci ga jikin dan Adam, da yake Azumi sahur ne yake maye gurbinsa. Ga mai azumi yana da kyau yake yin sahur domin zai taimakawa jikinsa wajen zama cikin inganci da bawa sassan jiki damar yin aiki yadda ya kamata tun daga yin sahur din har zuwa buda baki.[4]

  1. Rima Al-Mukhtar (10 August 2011). "Ramadan Mesaharati". Arab News. Retrieved 25 March 2023.
  2. "Qasida". Banglapedia. Retrieved 25 March 2023.
  3. "Tarihin tashe a ƙasar Hausa". BBC Hausa. 18 June 2017. Retrieved 25 March 2023.
  4. Ishaq, Mudathir (17 May 2018). "Abubuwa 10 da zasu kara muku lafiya yayin gudanar da Azumin Ramadan". Legit.Hausa.ng. Retrieved 25 March 2023.